Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 22:50:12    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Bayan kwanaki 12 da rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, a ran 6 ga wata da dare, an bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sanar da bude gasar, shugaba Philip Craven na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya yi jawabi a gun bikin budewar, inda ya ce, gasar wasannin Olympic ta Beijing na da kayatarwa sosai, ya yi imani da cewa, tabbas ne za a sami nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing.

A cikin jawabinsa, Mr. Craven ya ce, a cikin kwanaki 12 na gasar wasannin Olympic ta nakasssu ta Beijing, za ka gano cewa, a gaskiya kuma, wadannan bambanci da ke kasancewa a duniya a idonka ba su yi tsanani sosai ba.

A cikin dukkan mambobi 162 na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, wasu 147 sun aika da kungiyoyin 'yan wasa domin shiga gasar. Yawan 'yan wasan ya wuce dubu 4. Wadannan adadi 2 sun wuce na dukkan gasannin wasannin Olympic na nakasassu da aka yi a da. Ban da wannan kuma, yawan shirye-shiryen wasannin motsa jiki a wannan karo ya kai matsayin koli a tarihin gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

A cikin jawabinsa, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, gwamnatin Sin da jama'ar Sin suna goyon bayan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing sosai. Ana nuna fatan alheri kan ganin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta zama kasaitaccen biki na morewa da farin ciki da zumunci da buri da kuma nasara tare.

Wannan shi ne karo na farko da wani kwamitin shiryawa ya share fage da kuma gudanar da gasar wasannin Olympic da ta nakasassu a lokaci guda. Bayan samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2001, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da gwamnatin kasar Sin sun yi wa kasashen duniya alkawarin cewa, za su mayar da 'yin fice da haduwa da morewa' a matsayin babban taken gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, za su yi kokari domin ganin an yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai kayatarwa kamar yadda gasar wasannin Olympic take.(Tasallah)