Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 17:20:44    
Za a bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri
Bayan kwanaki 12 da rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, yau da dare wato ran 6 ga wata da dare, za bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai sanar da bude gasar, shugaba Philip Craven na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya zai yi jawabi a gun bikin budewar.

A cikin dukkan mambobi 162 na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, wasu 147 sun aika da kungiyoyin 'yan wasa domin shiga gasar. Yawan 'yan wasan ya wuce dubu 4. Wadannan adadai 2 sun wuce na dukkan gasannin wasannin Olympic na nakasassu da aka yi a da. Ban da wannan kuma, yawan shirye-shiryen wasannin motsa jiki a wannan karo ya kai matsayin koli a tarihin gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

Wannan shi ne karo na farko da wani kwamitin shiryawa ya share fage da kuma gudanar da gasar wasannin Olympic da ta nakasassu a lokaci guda. Bayan samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2001, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da gwamnatin kasar Sin sun yi wa kasashen duniya alkawarin cewa, za su mayar da 'wucewa da haduwa da morewa' a matsayin babban taken gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, za su yi kokari domin ganin an yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai kayatarwa kamar yadda gasar wasannin Olympic take.(Tasallah)