Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 16:58:31    
Shugaban kasar Sin ya shirya liyafa domin maraba da manyan baki

cri
Ran 6 ga wata da tsakar rana, a babban dakin taro na jama'a da ke nan Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da kuma matarsa sun shirya liyafa domin maraba da manyan baki da za su halarci gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing.

A cikin jawabin da ya yi a gun liyafar, shugaba Hu ya bayyana cewa, tun bayan da kasar Sin ta sami bakuncin shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a shekarar 2001 har zuwa yanzu, gwamnatin Sin da jama'ar Sin sun aiwatar da alkawarin da suka yi wa kasashen duniya a tsanake, sun yi iyakacin kokari wajen share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing bisa bukatar da aka bayar, wato shirya gasar wasannin Olympic da ta nakasassu masu kayatarwa. Ya yi imani da cewa, tabbas ne za a yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing mai halin musamman kuma bisa babban mataki. Sa'an nan kuma, a matsayinta na wani dandamalin da zai kyautata amincewa da juna da zumunci a tsakanin nakasassun da suka zo daga kasashe daban daban, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing za ta bai wa sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya dukiya mai daraja ta fuskar ruhu.

Ban da wannan kuma, shugaba Hu ya jaddada cewa, kasar Sin za ta yi amfani da damar shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing domin himmantuwa wajen kiyaye iko da moriyar nakasassu da tabbatar da ganin nakasassu sun shiga harkokin zaman al'ummar kasa cikin adalci da kuma more sakamakon da kasar Sin ta samu daga wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa.(Tasallah)