Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 21:18:38    
Kasar Sin za ta yi iyakacin kokari domin gudanar da gasar Olympic ta nakasassu a cewar Wen Jiabao

cri

Ran 5 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya gana da Mr. Waldemar Pawlak mataimakin firaministan kasar Poland wanda zai halarci bikin bude gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing. Mr. Wen Jiabao ya nuna cewa, kasar Sin za ta yi iyakacin kokari domin gudanar da gasar Olympic ta nakasassu kamar gasar Olympic mai kayatarwa da ta yi.

Mr. Wen Jiabao ya ce, gasar Olympic ta nakasassu ita ce wani dandalin inda nakasassu ke nuna hali mai nagarta da salon zamanin yanzu, kuma za ta sanya a kara mai da hankali kan sha'anin nakasassu.

Mr. Pawlak ya taya murna ga gwamnati da jama'ar kasar Sin a sakamakon ta cimma nasarar gudanar da gasar Olympic. Kuma ya nuna fatan alheri ga cikakkiyar nasarar gasar Olympic ta nakasassu.