Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 20:53:39    
An taya murna ga kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta karo na 13 a Beijing

cri
A ran 6 ga wata, za a yi bayanin edita a kan jaridar "People's Daily" ta kasar Sin, inda za a taya murna ga kaddamar da gasar wasannin Olympic ta karo na 13 a Beijing.

Wannan bayanin edita ya ce, a ran 6 ga wata da dare, za a daga tutar taurari 5 ta kasar Sin da tutar kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa a filin motsa jiki na kasar Sin, kuma za a kunna wutar yola da ke bayyana annashuwar nakasassu fiye da miliyan dari 6 na duk duniya. Wannan wuta za ta yi walkiya a duk duniya.

A waje daya kuma, wannan bayanin edita ya ce, a matsayin wani gagarumin biki, inda yawan kasashe da yankuna da 'yan wasa nakasassu da za su halarci wannan gasa mafi yawa a tarihin gasannin wasannin Olympic na nakasassu, 'yan wasa nakasassu fiye da dubu 4 da suka zo daga kasashe da yankuna 148 za su yi gasa a dakali daya cikin adalci. Wadannan gasannin wasannin Olympic dukkansu za su kasance tamkar gasanni masu ban sha'awa, kuma masu jawo hankulan jama'a. Jama'ar kasar Sin da suka shirya wata ingantacciyar gasar wasannin Olympic ta Beijing da ke bayyana halayen musamman cikin nasara suna da imanin samar wa duk duniya wata gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai jawo hankulan jama'a.

Bugu da kari kuma, wannan bayanin edita ya ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta samu cigaba sosai kan harkokin nakasassu, kuma ta samu yabo daga sauran kasashen duniya kwarai. (Sanusi Chen)