Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 12:51:23    
Kasar Sin ta samu taimakon kudi da kasashen ketare suka bayar kan bala'in girgizar kasa da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 1.919

cri
Bisa labarin da aka samu daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin an ce, bayan aukuwar babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichaun, ya zuwa ranar 27 ga watan Augusta, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, da ofisoshi, da kungiyoyin jakadanci da na consulana kasar da ke kasashen ketare sun samu taimakon kudi daga gwamnatoci, da kungiyoyi, da jama'a na kasashen waje da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 1.919.

An ce, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta riga ta isar da wadannan kudade cikin lokaci ga asusun banki na musamman da hukumomin gwamnati suka kafa, don samun taimakon kudi kan bala'in girgizar kasa na Wenchuan, ko bangarori daban daban da abin ya shafa da aka tabbatar, a waje daya kuma, ta sanar da yadda za a yi amfani da wadannan kudade. (Bilkisu)