Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 19:49:49    
Kasar Sin ta yi ta kara bai wa nakasassu tabbaci ta fuskar zaman al'ummar kasa

cri
Ran 4 ga wata, wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya sami labari daga hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin cewar, a shekarun baya, kasar Sin ta yi ta inganta karfin bai wa nakasassu tabbaci ta fuskar zaman al'ummar kasa, ta sami babban ci gaba a sha'anin ba da tabbacin zaman al'ummar kasa ga nakasassu.

Daga wani bangare ne an kiyasta cewa, yanzu kasar Sin tana aiwatar da dokoki fiye da 50 dangane da kiyaye iko da moriyar nakasassu. Sa'an nan kuma, dokokin da ke shafar samar wa nakasssu guraban aikin yi suna ta samun kyautatuwa, yawan nakasassun da suka samu aikin yi ya wuce kashi 80 cikin dari bisa jimlar nakasassu. Ban da wannan kuma, a wurare daban daban na kasar Sin, ana himmantuwa wajen kawar da shinge domin nakasssu, ana kuma raya birane 100 marasa shinge a duk kasar.

Bugu da kari kuma, an fadada fannonin da ke shafar bai wa nakasassu tabbacin zaman al'ummar kasa, naksassu fiye da miliyan 7 na kasar Sin sun sami tabbacin zaman al'ummar kasa ta hanyoyi daban daban. Bisa shirin da abin ya shafa, nan gaba kasar Sin za ta shigar da nakasassu cikin tsarin kasar Sin na ba da tabbacin zaman al'ummar kasa, za ta ba su taimako a matakai daban daban, za ta kuma kyautata matsayin irin wannan tabbaci da za ta bai wa nakasassun da suka dace.(Tasallah)