
A ran 4 ga watan da safe, bayan da mai mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na karshe Liu Zhengwei ya isa filin Long Men na birnin Luoyang, ya kunna wutar dake cikin takunya, daga nan aka kammala aikin mika wutar a birnin Luoyang na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin.

Birnin Luoyang zango na biyar ne da aka mika wutar ta hanyar al'adu, kuma zango na karshe ne da aka mika wutar kafin wutar ta iso birnin Beijing. Masu mika wutar 70 sun shiga wannan aiki, daga cikinsu da akwai nakasassu guda 9, sauransu mutanen ne da suka ba da taimako ga nakasassu. An mika wutar a filin dake gaban Kogun Long Men, inda aka gano kayan al'adu mai dogon tarihi na birnin Luoyang.(Asabe)
|