A ran 3 ga watan a birnin Beijing, kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya kira taron kwamitin aiwatar da harkokin wasannin Olympic, inda shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Liu Qi ya bayyana cewa, an gama ayyukan share fagen wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.
Liu Qi ya ce, yanzu, ma'aikatan wasannin Olympic na nakasassu da masu sa kai fiye da dubu 40 a shirye suke. Biranen Beijing, da Qingdao, da Hongkong sun riga sun gama ayyukan share fage a fanonni daban daban. Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing zai samar da kayayyakin gasa da na zama ga 'yan wasan nakasassu da za su shiga gasannin Olympic na Beijing. Ban da wannan kuma, kwamitin zai ci gaba da kokarinsa wajen bayar da labaru, da shirya bukukuwa al'adu kamar bikin bude wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, don tabbatar da cewa, zai ci nasarar yin wasannin Olympic na nakasassu.
Shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya Philip Craven ya nuna babban yabo ga ayyukan share fage da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ya yi. Ya bayyana cewa, kwamitin shirya wasannin Olympic ya samu nasara wajen share fage. Kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya tabbata cewa, dukkan wasannin Olympic na nakasassu za su gudana tare da nasara kamar wasannin Olympic na Beijing. Bugu da kari, ya hakake cewa, wasannin Olympic na nakasassu a wannan karo za su ci babbar nasara, kuma zai rubuta wani sabon shafin wasannin Olympic na nakasassu.(Asabe)
|