Ran 3 ga wata, manema labaru sun sami labari daga hukumar da abin ya shafa cewa, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta dauki masu aikin sa kai dubu 44, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna guda 27.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan mutanen da suka nemi zama masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta birnin Beijing ya kai fiye da dubu 900, kuma an dauki mutane dubu 44, kuma a cikinsu mutane kashi 90 cikin kashi dari sun taba zama masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympic ta Beijing. A lokacin gasanni, masu aikin sa kai za su yi aikin hidimar 'yan kallo da zirga-zirga da tsaro da dai sauransu.
Dadin dadawa, masu aikin sa kai na birnin Beijing dubu 400 za su cigaba da aikin hidimar amsa tambayoyi da fassarawa da daidaita matsalar gagawa. A lokacin gasanni, za su tsara 'yan kallo da masu aikin sa kai domin sa kaimi ga 'yan wasa.(Fatima)
|