Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 18:15:34    
Kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da ingancin abinci da magunguna a lokacin gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing

cri
A ran 3 ga wata, a gun taron manema labaru da hukumar sa ido kan abinci da magunguna ta kasar Sin ta saba shiryawa, madam Yan Jiangying, kakakin wannan hukuma ta bayyana cewa, a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, halin tabbatar da ingancin abinci da magunguna da kasar Sin ke ciki yana da kyau. Sabo da haka, a lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu, za a ci gaba da aiwatar da manufofin tabbatar da ingancin abinci da magunguna.

A gun wannan taron manema labaru, da farko dai, madam Yan Jiangying ta bayyana yadda ake yaki da magungunan sa kuzari. Ta ce, kasar Sin ta sami sakamako mai kyau wajen yaki da magungunan sa kuzari. A lokacin gasar wasannin Olympic, ba a samu matsalar da ke nasaba da aikin sa ido kan magungunan sa kuzari ko sau daya ba.

An bayyana cewa, a lokacin wasannin Olympic ta Beijing, an taba karbar mutane a tasoshin likitanci na dakuna da filayen motsa jiki fiye da sau dubu 20. A cikin dukkan magunguna da na'urorin likitanci, ba a samu matsalar inganci ko sau daya ba. A waje daya kuma, an samar da isassun magunguna cikin lokaci a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma ba a yi kuskure ko hadari ko kara ko sau daya ba.

Sabo da haka, hukumar sa ido kan ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da kwararan manufofin tabbatar da ingancin abinci da magunguna a lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu. (Sanusi Chen)