A ran 3 ga watan, an mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a birnin Dalian na lardin Liaoning.
Birnin Dalian birni na biyar ne da aka mika wutar, masu mika wutar 70 sun shiga aikin nan. An fara mika wutar a filin wasanni mai suna Xinghai, kuma a gama aikin nan a wurin shakatawa na kungurmin daji. Tsawon hanyar da aka bi da wutar ya kai kilomita 3.8.
Za a mika wutar wasannin Olympic na nakasassu ta hanyoyi biyu wato hanyar al'adu da ta zamani. Tun daga ran 29 ga watan Agusta, aka fara mika wutar a birane 11. A ran 5 ga watan Satumba, wutar za ta isa birnin Beijing, kuma a ran 6 ga watan da dare, za a kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu a gun bikin bude wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.(Asabe)
|