Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-02 19:47:40    
Za a yi kokari domin samar da ayyuka marasa shinge a birnin Beijing

cri

Ran 2 ga wata, yayin da Mr. Zhou Zhengyu mataimakin direkatan hukumar zirga-zirga ta birnin Beijing ke ganawa da manema labarun da suka kai ziyara ga motoci marasa shinge na kamfanin zirga-zirgar jama'a ta Beijing ya bayyana cewa, yayin da ake yin gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, za a kebe hanyoyi 16 na musamman na zirga-zirgar jama'a, kuma za a yi amfani da motocin bos-bos marasa shinge fiye da 500 a sakamakon gasanni, kuma za a yi amfani da sauran motocin bos-bos marasa shinge fiye da 2000 saboda samar da aikin hidima ga jama'a.

Ban da haka kuma, a cikin tashoshi fiye da 100 na jirgin da ke tafiya a karkashin kasa na Beijing, za a yi amfani da na'urori fiye da 100 domin daukar mutane, kuma za a tabbatar da fasinjojin da ke amfani da keken guragu za su iya shiga tashoshi ta hanyoyi marasa shinge.

Mr. Zhou Zhengyu ya ce, ba motocin taksi kawai ba, har ma jiragen da ke tafiya a karkashin kasa, da bos-bos na birnin Beijing za su samar da aikin hidimar zirga-zirga ba dare ba rana ga nakasassu da ke amfani da keken guragu idan akwai bukata.

Mr. Zhou Zhengyu ya nuna cewa, saboda gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, birnin Beijing ya sami cigaba wajen samar da aikin gidima ga nakasassu. Bayan an rufe gasar, za a cigaba da yin amfani da wadannan motoci da na'urori marasa shinge.