Yau 2 ga wata, an yi taron manema labarai na farko a cibiyar watsa labaran wasannin Olympic na nakasassu, wannan kuma ya nuna cewa, Beijing ta shirya sosai wajen karbar baki a gun wasannin Olympic na nakasassu.
An ce, an sake kawatar da cibiyar watsa labaran wasannin Olympic na nakasassu, wato an sauya abubuwan ado na wasannin Olympic zuwa na wasannin Olympic na nakasassu. Sa'an nan, a babban ofishin manema labarai, an sanya alamar rashin abubuwan cikas, a dakalin watsa labarai kuma, an kara hanyar rashin abubuwan cikas ga nakasassu.
Kauyen wasannin Olympic na nakasassu da aka bude a ran 30 ga watan Agusta, an gyara shi ne daga kauyen wasannin Olympic. Domin samar wa 'yan wasa nakasassu saukin shigowa da kuma fitowa, ana amfani da bene na daya zuwa na uku ne kawai a kowane gini. Sa'an nan kuma, an gyara hotel-hotel 16 da su zama rashin abubuwan cikas ga nakasassu.
Bayan haka, tun daga makon da ya gabata, bi da bi ne aka fara amfani da hanyoyin da aka kebe musamman domin wasannin Olympic na nakasassu. (Lubabatu)
|