
A ran 1 ga watan da karfe 10 da rabi da safe, an gama mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a birnin Shanghai.

Birnin Shanghai birni na uku ne da aka mika wutar wasannin Olympic na nakasassu. Duk tsawon hanyar da za a mika wutar ya kai kilomita 3.1. Goma daga cikin masu mika wutar nakasassu ne, sauransu mutane ne da suka yi kokarin ba da taimako ga sha'anin nakasassu.
A ran 2 ga watan, za a mika wutar a birnin Qingdao, a ran nan kuma, za a mika wutar a birnin Nanjing.(Asabe)
|