Ran 31 ga watan Agusta, an mika wutar gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a birnin Wuhan na lardin Hubei da na Changsha na lardin Hunan.
Birnin Wuhan shi ne birni na biyu da kungiyar nune-nunen kyakkyawan zamantakewar zamani ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Tsawon hanyar mika wutar yola a Wuhan ya kai kilomita 3, kuma gaba daya masu mika wutar yola 60 sun halarci wannan aiki.
Birnin Changsha birni na 3 ne da kungiyar nune-nunen al'adun kasar Sin ta mika wutar yola. Tsawon hanyar mika wuta a Changsha ya kai kilomita3, kuma gaba daya masu mika wuta 70 sun halarci wannan aiki, a ciki har da masu mika wuta na nakasassu 13.
Ran 1 ga watan Satumba, kungiyar nune nunen kyakkyawan zamantakewar zamani za ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a birnin Shanghai. Ran 2 ga watan Satumba, kungiyar nune-nunen al'adun kasar Sin za ta mika wutar a birnin Nanjing.(Fatima)
|