A ran 30 ga wata, a hukunce ne, an bude kauyen Olympics na nakasassu na Beijing na shekarar 2008, tawagar wakilai ta kasar Sin ta zama karo na farko na 'yan wasa da za su zama a wannan kauye, haka kuma ta zama ta farko da ta daga tutar kasa.
Shugaban tawagar wakilai ta gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta kasar Sin Mr. Wang Xinxian ya bayyana cewa, dukkan 'yan wasa na kasar Sin za su yi kokari sosai domin samun maki mai kyau, a sa'i daya kuma, za su ji dadi daga wasanni.(Danladi)
|