Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-30 18:56:19    
'Yan siyasa na kasashen waje sun yaba wa gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

A 'yan kwanakin baya, wasu 'yan siyasa na kasa da kasa sun yaba wa nasarar da kasar Sin ta samu wajen shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A ran 29 ga wata, darektan cibiyar nazarin manufofi wajen samun bunkasuwa ta kasar Senegal Mr. Ali Sow ya bayyana wa manema labaru cewa, shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing da kasar Sin ta gudana ba wani abin alfahari ga jama'ar kasar Sin kawai ba, har ma ya zama wata nasara da dukkan jama'ar duniya da ke kaunar zaman lafiya suka samu.

A ran nan kuma, 'dan majalisa na kasar Faransa Mr. Bernard Debre ya bayyana cewa, ta gasar wasannin Olympics, kasashen duniya sun kara sanin kasar Sin, kasar Sin kuma ta nuna babbar kwarewa a fannonin wasanni ta hanyar shirya bukukuwan bude da rufe gasar wasannin Olympics da tsara wasannin.(Danladi)