A ranar 30 ga wata, an mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing a birnin Shenzhen na lardin Guangdong, da birnin Huhehaote na jihar Mongoliya ta gida mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin.
Tsawon hanyar da aka bi kan mika wutar yola a birnin Shenzhen, ya kai kilomita uku, masu mika wutar sun kai 70, ciki kuma nakasassu sun kai kusan kashi 20 cikin dari.
Birnin Huhehaote na jihar Mongiliya ta gida, shi ne birnin kananan kabilu daya kawai da aka mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. Tsawon hanyar da aka bi a gun bikin ya kai kilomita 3.1, masu mika wutar da yawansu ya kai 70 sun halarci bikin. (Bilkisu)
|