Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-30 17:11:45    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Turkmenistan, da shugaban majalisar dokoki ta jama'ar kasar

cri
A ranar 29 ga wata da dare, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya komo kasar Sin daga birnin Ashkhabad, babban birnin kasar Turkmenistan, bayan da ya kawo karshen ziyarar aiki a kasar cikin nasara. Kafin haka kuma, daya bayan daya ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Turkmenistan Gurbanguly Berdymukhamedov, da kuma shugaban majalisar dokoki ta jama'ar kasar madam Akja Nurberdyyeva.

A lokacin da yake yin shawarwari tare da Mr. Berdymukhamedov, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Turkmenistan iri na zaman daidaiwa daida da nuna amincewa ga juna, da samun moriyar juna da nasara tare a cikin dogon lokaci, wannan ne manufar da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa tsayin daka. Kasar Sin na son yin kokari tare da Turkmenistan, don ciyar da kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu gaba kamar yadda ya kamata.

A wannan rana da yamma, Mr. Hu Jintao ya halarci bikin bayar da lambar girmamawa, inda aka bayar masa lambar girmamawa ta "Niyazov". (Bilkisu)