Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 16:24:16    
Za a kara yawan tikitocin kallon wasannin Olympic na nakasassu na Beijing

cri
A bisa yawan tikitocin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da aka saya, wani jami'in cibiyar sayar da tikitocin wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, watakila za a kara yawan tikitocin wasannin Olympic da za a sayarwa jama'ar kasar Sin, cikin hada da tikitocin filin wasannin motsa jiki na kasa mai siffar shekar tsuntsu, wato "Bird's Nest" da cibiyar wasan iyo mai siffar "Water Cube" da dai sauransu.

Wannan jami'i ya bayyana cewa, tun da aka fara sayar da tikitocin gasannin wasannin Olympic na nakasassu a ran 20 ga watan Yuni, mutane da yawa suna son sayen tikitocin. Bisa shiri na farko, ana shirya sayar da tikitoci dubu 850 ga jama'ar kasar Sin. Amma a bisa sabuwar kididdigar da aka yi, yawan tikitocin da za a sayar zai karu, kuma cibiyar sayar da tikitoci tana kyautata tsarin sayar da tikitocin don kara yawan tikitocin da za su sayar.(Asabe)