Yau 29 ga wata, da misalin karfe 9 na safe, an fara mika wutar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a mashahurin birnin Xi'an dake yammacin kasar Sin, kuma da misalin karfe 10 da mintoci 35, an gama mika wutar.
Bayan da aka yi bikin kunne wutar a hasumiyar kofar ta gabas ta babbar ganuwa ta zamanin da ta birnin Xi'an, an fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu bisa ganuwa ta zamanin da, a karshe dai, an yi bikin kashe wuta a yammacin kofar ganuwa ta da. Tsawon hanyar da aka mika da wutar ya kai kilomita 3.1, dukkan yawan masu mika wuta ya kai 70, a cikinsu guda 11 su nakasassu ne.
A ran 30 ga wata, za a mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a birnin Shen Zhen dake yankin musamman na tattalin arziki a lardin Guangdong dake kudu maso gabashin kasar Sin da hedkwatar jihar Mongolia ta gida wato Hohhot dake arewacin kasar Sin a lokacin daya.(Asabe)
|