Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 16:16:01    
Mutanen kasa da kasa sun yaba wa wasannin Olympics na Beijing

cri
A kwanakin nan, wasu mutanen masu kula da harkokin siyasa da motsa jiki sun yaba wa cikakkiyar nasarar da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta samu.

A ran 28 ga wata, Julio Cobos, mataimakin shugaban kasar Agentina ya buga waya ga Zeng Gang, jakadan Sin da ke kasar Agentina don taya murna ga kasar Sin da ta yi wasannin Olympics cikin nasara da kuma ta zama matsayi na farko mai samun lambobin zinariya mafi yawa a gasar. Mr Cobos ya ce, gagarumin bukukuwan budewa da rufe wasannin Olympics na Beijing sun burge duniya, kuma ayyukan tsara gasanni suna da kyau sosai. Kuma ya nuna godiya ga bangaren Sin da ya ba da hidima mai kyau ga 'yan wasan Agentina a lokacin wasannin Olympics na Beijing.

Gediminas Kirkilas, firayin ministan kasar Lithuania da Toomas Hendrik Ilves, shugaban kasar Estonia su ma sun yaba wa kasar Sin saboda ta shirya wasannin Olympics na Beijing cikin nasara.

Ban da wannan, yayin da wasu 'yan wasan Palesdinu suke ganawa da 'yan jarida a ran 28 ga wata, sun bayyana cewa, wasannin Olympics na Beijing zai kasance wani al'ajabin da ba za a sake ganinsa ba.(Zainab)