Ran 28 ga wata, wakilin jaridar People's Daily ta kasar Sin ya sami labari daga wani taron da aka yi a birnin Beijing cewa, masu aikin sa kai kimanin dubu 44 za su ba da hidima a cikin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing.
An labarta cewa, mutane fiye da dubu 900 sun yi rajistar neman zama masu aikin sa kai a cikin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Wadannan mutane dubu 44 da aka karbe su a matsayin masu aikin sa kai sun zo daga kasashe da yankuna 27. A cikin wadannan masu aikin sa kai, wasu da yawansu ya kai kashi 90 cikin dari sun riga sun yi aikin sa kai a cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing.
A lokacin gasar, wadannan masu aikin sa kai za su bayar da hidima ga 'yan kallo a fannonin zirga-zirga da ayyukan tsaro da kiwon lafiya da harsuna da gudanar da filayen wasa da taimakawa 'yan jaridu da kuma a cikin bukukuwan ba da lambobin yabo.(Tasallah)
|