Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 15:19:43    
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yaba wa gasar wasannin Olympics ta Beijing da ta ci nasara

cri

A kwanakin nan, kafofin watsa labaru da 'yan jarida na kasashen Panama da Burkina Faso da Combodia sun ba da sharhi da labaru don yaba wa nasarar da gasar wasannin Olympics ta Beijing da ta samu.

Kafofin watsa labaru na Burkina Faso sun taya murna ga wasannin Olympics na Beijing da kasar Sin ta yi cikin nasara da sakamako mai kyau da 'yan wasan Sin suka samu. Kafofin watsa labaru na Burkina Faso suna tsammani cewa, wasu kasashe masu ci gaba suna son hada da wasannin Olympics da siyasa, amma kasar Sin ta tsayawa tsayin daka a kanta a karkashin matsin siyasa mai karfi. Wasu kafofin watsa labaru na Burkina Faso suna tsammani cewa, kasar Sin ta burge duniya ta hanyar shirya wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008.

A cikin sharhin da jaridar El Panama America ta bayar, an ce, kasar Sin ta yi wasannin Olympics cikin nasara da kyawawan aikin hidima da gine-ginen filayen wasan motsa jiki na zamani da fitaccen aikin sa kai.(Zainab)