

Yau 29 ga wata, da misalin karfe 9 na safe, an fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a mashahurin birnin Xi'an dake yammacin kasar Sin.



Bayan da aka yi bikin kunna wutar a hasumiya ta gabashin kofar ganuwa ta da a birnin Xi'an, an fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu bisa ganuwa ta da, a karshe dai, za a yi bikin kashe wuta a yammacin kofar ganuwa ta da. Tsawon hanyar da za a mika wuta ya kai kilomita 3.1, dukkan yawan masu mika wutar ya kai 70, a cikinsu guda 11 su nakasassu ne.(Asabe)
|