Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 16:13:44    
An yi bikin kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a wurin Tian Tan

cri

A ran 28 ga wata da safe, an kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a wurin Tian Tan na birnin Beijing. Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanar da cewa, za a fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu a hukunce. Mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na Beijing Liu Qi, da kuma shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya Philip Craven sun halarci bikin kunna wutar yola ta wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.

A gun bikin, hugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na Beijing Liu Qi ya bayyana cewa, wutar wasannin Olympic na nakasassu za ta yada ra'ayoyin daidaituwa da abokantaka da ba da taimako ga juna a cikin jama'ar kasa da kasa, kuma za ta ciyar da bunkasuwar ayyukan nakasassu a duniya gaba.

Bugu da kari, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya Philip Cravenya bayyana cewa, kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu ya alamantar da cewa, wasannin Olympic a wannan karo ya soma a kasar Sin. 'Yan wasan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing za su yi kokari don samu sakamako mai kyau a cikin gasar wasannin Olympic.(Asabe)