Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 14:26:24    
Mutanen kasashen waje sun yaba wa gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

An rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing, amma mutanen kasa da kasa ba su manta da gagarumar gasar nan ba. Bayan da aka kammala gasanni masu ban sha'awa, mutanen duniya sun nuna yabo ga aikin shirya wasannin Olympics na Beijing.

Yayin da Koksal Toptan, shugaban majalisar dokokin kasar Turkey ya gana da Sun Guoxiang, jakadan Sin mai barin gado da ke a Turkey a ran 27 ga wata, ya bayyana cewa, jama'ar Sin sun shaida wa dunya da hakikan abubuwa cewa, wasannin Olympics na Beijing cikakke ne maras na biyu wajen tsara wasanni da shirya su.

Yayin da Nicholas Sarkozy, shugaban kasar Faransa ya gana da 'yan wasan Faransa a fadar shugaban kasa a kwanakin nan, ya bayyana cewa, wasannin Olympics na Beijing wani gagarumin biki ne, ba ma kawai yana da kyaun gani ba, hatta ma an karya matsayin duniya a fannoni da yawa.

A kwanakin nan, yayin da Irving Saladino, dan wasan dogon tsalle da ya samu lambar zinariya ta farko ga kasar Panama a tarihi ya yi hira da kafofin watsa labaru, ya yaba wa babban filin wasa na kasar Sin wato " shekar tsuntsu " da girma da kyaun gani, kuma hazikancin jama'ar Sin ya burge shi sosai.(Zainab)