Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 14:12:09    
Kasar Sin za ta kammala muhimman ayyukan farfado da yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a lardin Si Chuan cikin shekaru 3 masu zuwa

cri
A ran 27 ga wata a birnin Beijing, mataimakin direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhu Zhixin ya bayyana cewa, kasar Sin tana ci gaba da gina yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a lardin Sichuan, kuma za ta kammala muhimman ayyukan gina wadannan yankuna cikin shekaru uku masu zuwa.

A ran 12 ga watan Mayu na shekarar nan, an samu girgizar kasa mai karfin digiri 8.0 a lardin Si Chuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ya haddasa babbar hasarar rayuka da dukiyoyi. A gun wani taron da abin ya shafa, Mr. Zhu Zhixin ya gabatar da cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gama shirye-shiryen sake gina yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa, kuma tana neman shawarwari daga jama'ar kasar. Bugu da kari, za a yi ayyukan ba da agaji bisa ka'idar lardin daya ya ba da taimako ga gunduma daya. Dadin dadawa, an riga an tabbatar da samun larduna da birane 19 da za su ba da taimako wajen gina gidaje, da makarantu, da hukumomin kiwon lafiya, da manyan ayyuka, da kuma manyan ayyukan ba da hidima da dai sauransu.

An ba da labari cewa, yawan kudin da ma'aikatar kudi ta gwamnatin tsakiya ta kebe wajen farfado da yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa ya kai kudin Sin yuan biliyan 70. Yanzu, an fara wasu ayyukan farfado da wadannan yankuna.(Asabe)