Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 22:40:24    
Beijing ta bai wa mazaunanta shawarar sa hannu cikin wasannin Olympic na nakasassu da ba da nasu taimako

cri
Yau 27 ga wata, rana ce da ta rage sauran kwanaki 10 da fara wasannin Olympic na nakasassu, kuma sassan da abin ya shafa na birnin Beijing sun hada gwiwa sun bayar da takardar shawara, inda suka shawarci mazaunan birnin da su sa hannu cikin wasannin Olympic na nakasassu da ba da nasu taimako cikin himma.

Shawarar ta ce, ya kamata a fara ne daga taimaka wa nakasassu da ke kawayenka, a yi abuta da su. Sa'an nan, a kare kayayyakin da aka yi domin nakasassu, don samar musu saukin zama. Bayan haka, an kuma shawarci a je kallon wasannin Olympic na nakasassu, a karfafa gwiwar 'yan wasa, sa'an nan, a yi kokarin shiga aikin sa kai.(Lubabatu)