Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 21:36:21    
Sin ta amince da babban shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa da ya faru a gumdumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri

A ran 27 ga wata, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya shugabanci wani zaunannen taron majalisar gudanarwa, inda aka dudduba da kuma amincewa da babban shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa da ya faru a gumdumar Wenchuan ta lardin Sichuan bisa ka'ida.

Taron ya ce, bisa abubuwan da aka tanada cikin wannan babban shiri ne, za a yi amfani da shekaru 3 masu zuwa domin cim ma burin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa a fannonin zaman rayuwar jama'a da kuma tattalin arziki da zaman al'umma da su kai halin da ake ciki kafin girgizar kasa ko za su wuce shi, haka kuma an tabbatar da manyan ayyuka wajen sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa. Wannan babban shiri ya zama wani muhimmin tushe ne da ake bi wajen gudanar da ayyukan sake raya yankunan, wanda zai bayar da jagora mai muhimmanci wajen gaggauta samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, da sake gina gidaje masu kyau a yankunan masu fama da girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.(Danladi)