Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 19:56:50    
Jama'ar kasa da kasa sun nuna yabo ga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

An riga an rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing. A 'yan kwanakin baya, jama'ar kasa da kasa da yawa sun yaba wa ayyukan da kasar Sin ta yi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A yayin da yake zantawa da babbar jaridar 'Dinamani' ta kasar Mexico, shugaba mai girmamawa na hukumar wasannin Olympics ta duniya Mr. Juan Antonio Samaranch ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing ita ce mafi kyau a tarihin Olympics da ya gani. Kasar Sin ta gudanar da kyawawan ayyukan tsara wasannin, da kuma bayar da na'urori masu kyau. Tagawar wakilai ta kasar Sin ta samu maki mai kyau, a sa'i daya kuma, dukkan jama'ar kasar Sin sun shiga ayyukan shirya wasannin, sun nuna himma sosai kan haka.

A ran 26 ga wata da dare, yayin da Nicholas Sarkozy, shugaban kasar Faransa ya gana da 'yan wasa masu halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing a fadar shugaba, ya bayyana cewa, wasannin Olympics na Beijing shi ne wani gagarumin biki, kuma 'yan wasa sun karya matsayin bajinta da yawa.

Ban da wannan kuma, jama'ar sauran kasashe kamar Canada, da Mongoliya, da Panama, da Austria, da Mexico da dai sauransu sun yaba wa gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)