Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 17:21:15    
Kanfanin watsa labaru na kasar Congo Brazzaville ya yaba wa gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

A ran 26 ga wata, jaridar "Les Depeches De Brazzaville" ta bayar da bayanin edita cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zama gasar mafi kyau a tarihi.

Bayanin edita mai suna "Hakikan Abubuwan" ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zama gasar wasannin Olympic mafi kyau, da girma, da kuma kyakkyawan shirya, shi ya sa, ta zama gasar mafi kyau wajen shaida wa mutane karfin kasa. Ta gasar wasannin Olympic ta Beijing, mutane sun canja ra'ayoyinsu game da kasar Sin, mutanen kasashen waje sun kara fahimtar da ainihin hali da kasar Sin ke ciki.

A cikin bayani, an ce, burin wadansu mutane da suka neman shafa bakin fenti ga gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bi ruwa. Duk wanda yake gurbata aikin mika wutar gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympicya yi hassara. (Zubairu)