A ran 26 ga wata da dare, yayin da Nicholas Sarkozy, shugaban kasar Faransa ya gana da 'yan wasa masu halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing a fadar shugaba, ya bayyana cewa, wasannin Olympics na Beijing shi ne wani gagarumin biki, kuma ya taya murna ga 'yan wasan Faransa da suka samu maki mai kyau a gasar.
Sarkozy ya ce, ba ma shirin aikin wasannin Olympics na Beijing yana da kyau kawai ba, hatta ma an samu sakamako mai kyau a gasanni da yawa. A kasar Faransa kuma, duk jama'a sun ji dadi sosai a kan wasannin Olympics na wannan karo.
Sarkozy ya taya murna ga dukan 'yan wasan Faransa. Ya ce, 'yan wasan Faransa sun samu lambobi 40 a gasar wasannin Olympics ta Beijing, kuma jama'ar Faransa sun ji dadi da alfarma a kan su.
Sarkozy ya fadi cewa, kasar Ingila ta samu sakamako mai kyau a gasar, kuma yana fatan kasar Faransa za ta tsamo darussa daga ita don samu maki mai kyau a gasar wasannin Olympics ta London a shekarar 2012.(Zainab)
|