Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 21:22:55    
Kasar Sin tana fata kada kasar Amurka ta dauki ma'aunoni biyu a kan hakkin 'dan Adam

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mr. Qin Gang ya bayyana a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 26 ga wata a birnin Beijing cewa, kasar Sin tana fata kada kasar Amurka ta dauki ma'aunoni biyu a kan hakkin 'dan Adam.

A 'yan kwanakin baya, wani jami'in fadar White house ta kasar Amurka ya kai suka kan hakkin 'dan Adam na kasar Sin a gasar wasannin Olympics. Game da haka, Mr. Qin ya nuna rashin jin dadi. Ya ce, har kullum gwamnatin kasar Sin tana dukufa wajen tabbatar da hakkin 'dan Adam na jama'ar kasar Sin. Kokarin da kasar Sin take yi wajen sa kaimi ga bunkasuwar hakkin 'dan Adam bai fara ne daga gasar wasannin Olympics ba, haka kuma ba zai daina ba sakamakon rufe wasannin Olympics. Mr. Qin ya ci gaba da cewa, tsarin mulki na kasar Sin ya tabbatar da kuma sa kaimi ga sha'anin hakkin 'dan Adam. Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen cim ma wannan buri.(Danladi)