|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-26 20:22:38
|
Nasarar da aka samu wajen shirya wasannin Olympics na kara fahimtar juna, da sada zumunta a tsakanin Sin da kasashe daban daban
cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana yau 26 ga wata a nan birnin Beijing cewa, shirya wasannin Olympics cikin nasara da kasar Sin ta yi na kara fahimtar juna, da sada zumunta a tsakaninta da kasashe daban daban na duniya, kazalika kuma ya sanya kasashe daban daban da su kara fahimtar kasar Sin a dukkan fannoni.
Mr. Qin Gang ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana. Ya ce, kasar Sin wata babbar kasa ce mai tasowa. Tana son yin kokari tare da jama'ar sauran kasashe daban daban na duniya, don bayar da taimako kan tabbatar da zaman lafiya, da samun bunkasuwa da wadatuwa tare. (Bilkisu)
|
|
|