Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 18:05:18    
Kafofin watsa labaru na ketare sun yabawa gasar Olympic ta Beijing tana da ma'anar tarihi sosai

cri

Bayan an rufe gasar Olympic ta Beijing, a cikin kwanakin baya, kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun yi rahotanni da yawa, inda suka yaba ayyukan shirya gasar Olympic ta Beijing cewa babu aibi ko kadan, kuma bikin budewa da bikin rufewa masu kayatarwa da kyakkyawan sakamakon da 'yan wasan kasar Sin suna samu sun nuna karfin kasar Sin, suna da ma'anar tarihi sosai.

A ran 25 ga wata, bi da bi ne wasu jaridun kasar Coet d'Ivoire sun bayar da bayyanin cewa, ayyukan shirya gasar Olympic ta Beijing ba su da aibi ko kadan.

Jaridar "New Vision" ta gwamnatin kasar Uganda ta yi sharhi cewa, kasar Sin ta nuna karfinta a matsayin wata kasa ta gabas mai dogon tarihi, da fasahohi masu cigaba na yin gasanni.

A ran 25 ga wata, dukkan manyan jaridun kasar Birtaniya sun bayar da labarin rufewar gasar Olympic ta Beijing da babban hotunan bikin rufewa.

Ban da haka kuma, manyan kafofin watsa labaru na kasashen Amurka, da Faransa, da Afirka ta kudu, da New Zealand, da Mexico, da Kenya sun yi rahotanni kan ayyukan shirywa gasar Olympic ta Beijing.