A 'yan kwanakin baya, shahararrun mutanen ketare da shugabannin kasashen waje da yawa sun bi hanyoyi daban daban, sun taya murna ga kasar Sin wajen samun nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, sun yaba wa taimakon da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka yi domin hakan.
Shugaban kasar Niger Mr. Mamadou Tandja ya bayyana a ran 25 ga wata cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing ta fi samun nasara a tarihi, wannan dai ya bayyana wa kwarewar gwamnatin kasar Sin da jama'arta, wannan kuma ya zama nasara da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka samu wajen daidaita matsaloli da dama, da kuma wani sakamakon da suka samu na nuna kishin kasarsu.
Ban da shi kuma, babban sakataren MDD Mr. Ban Ki-moon, da kuma shugaba mai girmamawa na duk rayuwarsa na hukumar wasannin Olympics ta duniya Mr. Samaranch su ma sun yaba wa gasar wasannin Olympics ta Beijing, sun ce, wannan gasa ta fi kyau a tarihin wasannin Olympics.(Danladi)
|