|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-25 20:21:54
|
 |
Hukumar wasannin Olympics ta duniya ta bayar da lambobin girmamawa na Olympics ga Liu Qi, da sauran mutane
cri
A ranar 25 ga wata a hotel na Beijing, hukumar wasannin Olympics ta duniya ta shirya liyafar abincin safe don nuna godiya, inda aka bayar da lambobin girmamawa na Olympics. Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren kwamitin birnin Beijing, kuma shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing Mr. Liu Qi, ya samu lambar girmamawa ta zinariya ta Olympics. Kazalika kuma, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara a fannin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing Deng Pufang, da kuma sauran mutane 13 sun samu lambobin girmamawa na azurfa na Olympics.
A gun bikin bayar da lambobin girmamawa, shugaban hukumar wasannin Olympics ta duniya Jacquce Rogge ya yi jawabi cewa, gasar wasannin Olympics ta wannan karo, wata gagarumar gasar wasannin Olympics ce. Ya yi godiya ga iyakacin goyon baya da jama'ar kasar Sin, da kwamitin shirya wasannin Olympics suka nuna, kuma ya yi godiya ga dukkan mambobi babban iyalin Olympics na duniya.
Mr. Liu Qi ya ce, ba kawai lambobin girmamawa na Olympics da aka bayar su ne, yabo da aka nuna ga kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ba, har ma su ne tabbaci da yabo da aka bayar ga jama'ar kasar Sin wajen shirya gasar wasannin Olympics ta wannan karo cikin nasara. (Bilkisu)
|
|
|