Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 17:25:23    
Shugabannin Sin da Korea ta kudu sun yi shawarwari da juna

cri

Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Korea ta kudu Mr. Lee Myong Bak a ran 25 ga wata a birnin Seoul, babban birnin kasar Korea ta kudu.

Da farko dai, Mr. Hu ya ce, bisa goyon baya daga kasashen duniya ciki har da kasar Korea ta kudu, kasar Sin ta samu nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing. Gwamnatin kasar Sin ta nuna godiya ga gwamnatin kasar Korea ta kudu da kuma jama'arta. Ban da wannan kuma, Mr. Hu ya taya murna ga maki mai kyau da 'yan wasa na kasar Korea ta kudu suka samu a gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mr. Hu ya ci gaba da cewa, a cikin shekaru 16 da kasashen biyu suka kulla dangantakar diplomasiyya, dangantakarsu tana samun bunkasuwa a fannoni daban daban, wannan kuma ya samar da moriya ga jama'ar kasashen biyu, da bayar da taimako ga shimfida zaman lafiya da albarka a shiyyarsu.

Mr. Lee Myong Bak ya ce, ziyarar da shugaba Hu ya kai wa kasar Korea ta kudu a lokacin cikon shekaru 16 da kafuwar dangantakar diplomasiyya da ke tsakaninsu tana da wata muhimmiyar ma'ana, ya taya murna ga kasar Sin wajen samun nasarar yaki da bala'un girgizar kasa a lardin Sichuan da kuma shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, da samu maki mai kyau a wannan gasa. Yana fatan kara raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin shawarwari na wannan karo.(Danladi)