Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 21:48:00    
Jaridar 'People's Daily' za ta buga bayani don taya murnar rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta karo na 29

cri

Jaridar 'People's Daily' ta kasar Sin da za ta buga bayani a ran 25 ga wata za ta bayar da wani sharhi, domin taya murnar rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta karo na 29.

Sharhin zai fadi cewa, kasashe da yankuna 204, da 'yan wasa fiye da dubu 10, da 'yan kallo biliyan 4.5 sun shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing, sabo da haka ne, gasar ta zama gasar Olympics da ta fi samun yawan kasashe da yankuna da suka halarta, da kuma aka fi watsa labaru game da ita a tarihin wasannin Olympics.

Sharhin zai ce, tare da alkawarin shirya gasar wasannin Olympics da ke da abubuwan musamman, da kuma ke da matsayi mai kyau, jama'ar kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.3 sun yi kokari da suke iya yi da kuma nuna himma da suke iya, domin samar da wani dandali na jin dadi ga 'yan Adam, da kuma bude wata kofar fahimtar juna ga kasar Sin. Ra'ayoyin wasannin Olympis na kyakkyawan muhalli, da wasannin Olympics na kimiyya da fasaha, da wasannin Olympics na al'adu za su bayar da wani muhimmin tasiri a yunkurin zamanintar da kasar Sin.(Danladi)