Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 20:12:00    
An soma bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Da misalin karfe 8 na yau da dare an soma bikin rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 da aka yi a Beijing. A gun wannan gasar Olympic, yawan kasashe da yankuna da yawan sabbin matsayin bajinta da aka kafa da yawan awoyin shirye-shiryen rediyo da na talabijin da aka watsa wa duk duniya da yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen gasannin wasannin Olympic na Beijing, dukkansu sun kafa sabbin matsayin bajinta a tarihin gasannin Olympic.

A cikin gasannin wannan gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasa da suka samu lambobin yabo sun zo daga kasashe da yankuna fiye da 80, wato ya wuce adadi na 75 na gasar wasannin Olympic ta Athens. Wannan ya almanta cewa, makin da 'yan wasa suka samu a gun wasannin Olympic ya samu daidaito a tsakanin membobin Olympic.

A kan dakalin lambobin zinariya, a karo na farko ne kasar Sin ta hau kan mukami na farko, kasar Amurka tana biye, sannan kasar Rasha tana ta uku. Amma a gun dakalin jimlar yawan lambobin yabo da aka samu, kasar Amurka tana matsayin farko kamar a da.

Wannan ne karo na fako da aka shirya gaggarumin bikin wasannin motsa jiki mafi girma a duniya a kasar da take da mutane mafi yawa. A gun bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a yi yau da dare, birnin London na Britaniya zai karbi tutar Olympic mai zobba 5 daga hannun birnin Beijing domin gasar wasannin Olympic ta shekarar 2012.

Bayan labarun duniya na wannan lokaci, za mu gabatar muku da wani shirin musamman game da bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing. Muna fatan za ku kebe lokaci ku saurari wannan shirin da muka tsara muku na musamman. (Sanusi Chen)