|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-08-24 19:18:23
|
Kokarin da kasar Sin ke yi wajen shirya gasar wasannin Olympics ba ya lalacewa, a cewar firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao
cri
A ranar 24 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, ba kawai kasar Sin ta samar da dama ta hanyar shirya wasannin Olympics ga 'yan wasa daga kasashe daban daban, don su nuna kwarewarsu ba, har ma ta nuna sabon halin da take ciki ga duk duniya. Kokarin da kasar Sin ke yi kan wasannin Olympics ba ya lalacewa, kasar Sin kuma ta gamsu da wannan.
Mr. Wen Jiabao ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Dominica Roosevelt Skerrit a wannan rana.
Mr. Wen Jiabao ya ce, kasar Sin ta samu goyon baya daga kasashen duniya a fannoni daban daban a lokacin wasannin Olympics, kuma ta yi godiya kan wannan. (Bilkisu)
|
|
|