Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 19:11:53    
Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na Burundi da Indonisiya

cri

A ran 24 ga wata a birnin Beijing, bi da bi ne, mataimakin shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasar Burundi Mr. Gabriel Ntisezerana, da kuma na kasar Indonisiya Mr Yusuf Kalla.

A ganawarsa da Ntisezerana, Mr. Xi ya nuna godiya ga kasar Burundi da ta nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. Mr. Xi ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan zumuncin gargajiya da ke tsakaninta da kasar Burundi, tana son yin kokari tare da Burundi, domin kara raya dangantakarsu. Mr. Ntisezerana ya taya murna ga birnin Beijing wajen shirya gasar wasannin Olympics cikin nasara. Ya ce, gwamnatin kasar Burundi za ta ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A ganawarsa da Kalla, Mr. Xi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indonisiya abokai ne bisa manyan tsare tsare, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Indonisiya, domin kara hada kansu bisa manyan tsare tsare da bayar da sabon taimako wajen shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a shiyyarsu da duk duniya. Mr. Kalla ya taya murna ga birnin Beijing wajen shirya gasar wasannin Olympics cikin nasara, ya ce, wannan ya zama abin alfahari ne ga dukkan jama'ar Asiya. Ya ci gaba da cewa, kasar Indonisiya tana son kara raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare da ke tsakanin kasashen biyu.(Danladi)