Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 16:55:48    
Hu Jintao ya kira liyafar rana ga gaggan baki na kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

A ran 24 ga wata da tsakiyar rana a dakin Fangfei na babban masaukin baki na Diaoyutai, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kira liyafar rana, domin nuna maraba ga gaggan baki na kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mr Hu Jintao ya ce,

'Gasar wasannin Olympics ta Beijing ta yada ra'ayoyin Olympics na zaman lafiya, da sada zumunta, da hadin kai, gasar kuma ta zama wani gaggarumin biki da jama'ar kasa da kasa suka kalli da kuma halarci wasanni da kuma yin mu'amalar al'adu. Shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing zai kara sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin wasanni na kasar Sin, zai inganta yin mu'amala da hadin kai da ke tsakanin kasar Sin da sauran mambobin iyalan Olympics, haka kuma zai kara sa kaimi ga fahimtar juna da sada zumunta da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da ta duk duniya.'

Mr. Hu Jintao ya ci gaba da cewa, a 'yan kwanaki masu zuwa, za a bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing, kasar Sin za ta dauki ma'auni daya, domin shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu da ke da matsayi mai kyau, da kuma ke da abubuwan musamman, ta yadda kasar Sin za ta kara bayar da taimako ga bunkasuwar wasannin Olympics na duk duniya.(Danladi)