A cikin zagayen karshe na wasan kwallon kafa na maza na Olympics da aka yi a ran 23 ga wata da tsakar rana bisa agogon Beijing, kungiyar kasar Argentina ta lashe kungiyar kasar Nijeriya da ci daya da babu kome, ta haka kungiyar kasar Argentina ta zama zakara a cikin wasan kwallon kafa na maza, kuma kungiyar kasar Nijeriya ta samu lambar azurfa.
Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin kasashen biyu sun gamu da juna a cikin zagayen karshe na wasan kwallon kafa na maza na Olympics. A cikin zagayen karshe na wasan da aka yi a gun gasar wasannin Olympics ta Atalant ta shekara ta 1996, kungiyar kasar Nijeriya ta lashe kungiyar kasar Argentina, ta zama zakara.(Kande Gao)
|