Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-23 17:25:22    
Mr. Wen Jiabao ya gana da bakin kasashen waje da suka zo domin halartar ayyukan gasar Olympic ta Beijing

cri

Ran 23 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya gana da Mr. Gediminas Kirkilas firaministan kasar Lithuania, da Mr. Ivars Godmanis firaministan kasar Latvia, da Mr. Yves Leterme firaministan kasar Belgium.

Yayin da Mr. Wen Jiayao ke ganawa da Mr. Kirkilas, ya ce, kasar Sin tana son kara yin musanya tsakanin manyan jami'ai tare da kasar Lithuania, da kuma kara sa kaimi ga bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu bisa ka'idar girmamawa juna da moriyar juna.

Yayin da yake ganawa da Mr. Godmanis, Mr. Wen Jiabao ya nuna cewa, kasar Sin tana son kara yin shawarwari kan matsayi dabam daban a tsakanin kasashen Sin da Latvia, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da ciniki, da kara yin hadin gwiwa kan fannonin zirga-zirga da sauran fannoni, da sa kaimi ga musanyar tsakanin matasa.

Yayin da Mr. Wen Jiabao ke ganawa da Mr. Leterme, ya ce, kasar Belgium tana tsayawa tsayin daka kan ka'idar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ta daidaita batutuwan da suke shafar Taiwan, da Tibet, kasar Sin ta yabawa mata.

Ban da haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya gana da Madam Elaine Lan Chao shugaban kungiyar wakilan shugaban kasar Amurka kuma ministan 'yan kwadago da Mr. Michael Levitt ministan kiwon lafiya na kasar Amurka. Ya ce, ya kamata kasashen Sin da Amurka su cigaba da gudanar da muhimmiyar manufa ta yin hadin gwiwa mai dacewa, da moriyar juna gaba daya, da kara sada zumunci da yin hadin gwiwa, da kuma daidaita sabane-sabane da batutuwan da ke jawo hankulansu daga matsayin manyan tsare-tsare da hangen nesa, ta haka domin sa kaimi ga bunkasuwa mai dorewa ta huldar da ke tsakaninsu yadda ya kamata.