Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-22 22:04:50    
Kasar Nijeriya ta samu lambobin tagulla biyu

cri

Yau ranar 22 ga wata ne aka shiga kwana na 14 da soma gasar wasannin Olympics, za a fitar da lambobin zinariya 21 a wannan rana. Ya zuwa karfe 9 na dare bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 15. Kasar Nijeriya ta samu lambobin tagulla biyu.

A cikin gasar tseren kwale-kwale ta mita 1000 tsakanin maza biyu biyu, kungiyar 'yan wasan kasar Jamus ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar tseren kwale-kwale ta mita 1000 tsakanin maza hudu hudu, kungiyar 'yan wasan kasar Belorussia ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar gudu ta mita dubu 5 ta mata, 'yar wasa ta kasar Habasha Tirunesh Dibaba ta samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, a cikin gasar dogon tsalle ta mata, 'yar wasa ta kasar Nijeriya Okagbare Blessing ta samu lambar tagulla. 'Yar wasa ta kasar Brazil Maggi Higa ta samu lambar zinariya.

Kuma a cikin gasar gudu ta ba da sanda tsakanin mata hudu na mita 4, kungiyar 'yan wasan kasar Nijeriya ta samu lambar tagulla. Kungiyar kasar Rasha ta samu lambar zinariya.