A cikin shekaru 7, wato daga an ci nasarar samu damar shirya gasar wasannin Oympic zuwa gasar wasannin Olympic ta fara, ma'aikatar kimiyya da fasaha na kasar Sin, da birnin Beijing, da sauran hukumomi da abin ya shafa sun zuba jari da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 3.17, sun gama ayyuka sama da dubu, kuma sun samu sakamako mai kyau sosai.
A gun bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, an yi amfani da tsarin kimiyya da fasaha mafi wuya a tarihin gasar wasannin Olympic, an yi amfani da kimiyya da fasaha mafi zamani da yawa. Gidan wasa na "Birds Nest" da cibiyar wasannin ruwa na "Water Cube" sun fi kome a fannoni daban daban. A cikin duk sababbin gidajen wasannin Olympic guda 11 da aka kafa, cikin har da wurin shakatawa na Olympic, bangaren Sin ya tsara fasalin gidaje 7 da kansa, sauran 4 kuma bangaren Sin ya shirya su tare da kasashen waje. An samu sakamakon kimiyya da fasaha fiye da 10 wadanda kasar Sin ta yi aikin kirkira da kanta wajen gina gidajen wasannin Olympic. Ban da wannan kuma, duk bakin karfe da aka yi amfani da su a gidajen wasannin Olympic kirar Sin ne.
Rahoton kimantawa na kwamitin wasannin Olympic na duniya ya kimanta cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta bai wa kasar Sin da duk duniya wani kayan tarihi mai daraja sosai. (Zubairu)
|