Bisa iznin da babban kwamandan yaki da bala'in girgizar kasa da ceto na majalisar gudanarwa ya bayar, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ya sanar da cewa, ya zuwa ran 21 ga wata da misalin karfe 12, an riga an tabbatar da hasarar rayukan mutane 69226, kuma mutane 374643 sun ji rauni, mutane 17923 sun bace.
Bisa rahoton hukumar harkokin jama'a, an ce, ya zuwa ran 21 ga wata da misalin karfe 12, gaba daya darajar kudin agaji da kayayyaki da mutanen Sin da na kasashen duniya suka bayar ta kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 59.2.
Bisa rahoton hukumar kudade, ya zuwa ranar 21 ga wata da misalin karfe 12, gwamnatoci bisa matsayi dabam dabam na kasar Sin sun zuba kudin Sin yuan fiye da biliyan 66.9 ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto.(Fatima)
|